Dandalin Halal na Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Contact Us Publications Languages
Menene Allah Yake Bukata a Garemu? Darasi na 15Talifa na bayaTalifi na gaba

Taimaka Wa Wasu Su Yi Nufin Allah

Me ya sa za ka gaya wa wasu abin da ka ke koyo? (1)
Su wanene za ka gaya wa bisharar? (2)
Ta yaya halinka zai shafe wasu? (2)
Yaushe ne za ka iya wa’azi tare da ikklisiya? (3)

1. Zuwa yanzu, ka riga ka koya kyawawan abubuwa da yawa daga Littafi Mai-Tsarki. Wannan sanin ya kamata ya kai ka ga gina halayen Kirista. (Afisawa 4:22-24) Irin wannan sanin yana da muhimminci domin ka sami rai madawwami. (Yohanna 17:3) Amma dai, wasu ma suna bukatar su ji bisharar don su ma su tsira. Tilas ne dukan Kiristoci na gaskiya su yi ma wasu wa’azi. Umurnin Allah ne.—Romawa 10:10; 1 Korinthiyawa 9:16; 1 Timothawus 4:16.

2. Za ka iya somawa ta wurin gaya ma waɗanda suke kusa da kai abubuwa masu kyau da ka ke koya. Ka faɗe su ga iyalinka, abokananka, abokan makarantanka, da abokan aikinka. Ka yi haka da tawali’u da kuma haƙuri. (2 Timothawus 2:24, 25) Kuma ka tuna cewa mutane sun fi lura da halin mutum fiye da sauraran abin da yake faɗa. Saboda haka, kyakkyawan halinka zai iya jawo wasu su saurare saƙon da ka ke faɗa masu.—Matta 5:16; 1 Bitrus 3:1, 2, 16.

3. A hankali, za ka kai ka fara yin wa’azi tare da ikklisiyar Shaidun Jehovah da ke yankinka. Wannan muhimmiyar hanya ce a ci gabanka. (Matta 24:14) Dubi irin abin farin cikin da zai zama idan ka taimake wani ya zama bawan Jehovah kuma ya sami rai madawwami!—1 Tassalunikawa 2:19, 20.

 

An Wallafa a Shekara ta 1996

GidaSamaTalifa na bayaTalifi na gaba

Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.