| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 14 |
Yadda Aka Tsara Shaidun Jehovah |
|
| Yaushe Shaidun Jehovah na zamani suka soma? (1) | |
| Ta yaya ake gudanar da taro na Shaidun Jehovah? (2) | |
| Ta yaya ake samun kuɗaɗe da ake amfani da su? (3) | |
| Su wanene suke ja-gora a kowace ikklisiya? (4) | |
| Waɗanne manyan taro ne ake yi kowace shekara? (5) | |
| Waɗanne ayyuka ne ake yi a hedkwatarsu da kuma ofisoshin rassansu? (6) | |
1. Shaidun Jehovah na zamani sun soma ne a cikin shekara ta 1870. Da farko, ana kiransu Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki. Amma a 1931 sun canja zuwa suna na Nassi Shaidun Jehovah. (Ishaya 43:10) Daga ɗan kaɗan da farko, ƙungiyar ta yi girma zuwa miliyoyin Shaidu, waɗanda sun shagala suna aikin wa’azi a ƙasashe sama da 230.
2. Yawancin ikklisiyoyin Shaidun Jehovah suna taruwa sau uku kowane mako. An gayyace ka ka halarci kowanne cikinsu. (Ibraniyawa 10:24, 25) Littafi Mai-Tsarki ne tushen abin da ake koyarwa. Ana fara taro da kuma rufe taron da addu’a. Ana rera daga zuci ‘waƙoƙi na ruhaniya’ a yawancin taron. (Afisawa 5:18, 19) Ana halarta kyauta, ba a karɓan kuɗi.—Matta 10:8. 3. Yawancin ikklisiyoyi suna taruwa ne a cikin Majami’ar Mulki. Waɗannan dai gine-gine ne masu sauƙi da Shaidu da suka ba da kai suka gina. Ba za ka ga sifoffi ba, gicciye, ko kuwa abubuwa makamancin waɗannan cikin Majami’ar Mulki. Ana biyan bukatu na kuɗi ta wurin kyauta ta son rai. Ga waɗanda suke son su ba da kyauta, da akwai asusu da ake sa kyauta a ciki.—2 Korinthiyawa 9:7.
4. A cikin kowace ikklisiya, akwai dattiɓai, ko kuwa masu kula. Suna ja-gora wajen koyarwa a ikklisiya. (1 Timothawus 3:1-7; 5:17) Bayi masu hidima suna taimakonsu. (1 Timothawus 3:8-10, 12, 13) Ba a ɗaukaka waɗannan maza fiye da sauran mutanen ikklisiyar ba. (2 Korinthiyawa 1:24) Ba a ba su wasu laƙabi na musamman ba. (Matta 23:8-10) Ba sa ado da ya bambanta daga sauran jama’a. Ba a kuma biyansu aiki da suke yi. Da son rai dattiɓan suke kula da bukatun ruhaniya na ikklisiya. Suna yin ta’aziya kuma suna ba da ja-gora a lokuttan damuwa.—Yaƙub 5:14-16; 1 Bitrus 5:2, 3. 5. Shaidun Jehovah suna yin manyan taro ko kuwa taron gunduma kowace shekara. A waɗannan lokutta, ikklisiyoyi da yawa sukan haɗu don tsari na musamman na koyarwa daga Littafi Mai-Tsarki. Yin ma sababbin almajirai baftisma sashe ne na kullum a tsarin ayyukan kowane babban taro ko kuwa taron gunduma.—Matta 3:13-17; 28:19, 20. 6. Hedkwatar Shaidun Jehovah na dukan duniya tana New York. A can Hukumar Mulki take, rukunin riƙaƙƙun dattiɓai ne waɗanda suke lura da ikklisiyoyi na dukan duniya. Da akwai ofisoshin rassa sama da 100 a dukan duniya. A waɗannan wurare, waɗanda suka ba da kansu suke buga littattafai kuma suke aikawa da littattafan Littafi Mai-Tsarki. Anan kuma ake ja-gorar tsarin aikin wa’azi. Me ya sa ba za ka shirya ka ziyarci ofishin reshe da ke kusa da kai ba?
|
|||
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|