| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 12 |
Daraja Rai da Kuma Jini |
|
| Yaya ya kamata mu ɗauki rai? (1) zubar da ciki? (1) | |
| Ta yaya Kiristoci za su nuna sun damu da kiyaye lafiyarsu? (2) | |
| Yana da kyau ne a kashe dabbobi? (3) | |
| Waɗanne ayyuka ne ba sa daraja rai? (4) | |
| Menene dokar Allah game da jini? (5) | |
| Wannan ya haɗa da karɓan jini ne? (6) | |
1. Jehovah shi ne Tushen rai. Ran dukan abubuwa na Allah ne. (Zabura 36:9) Rai yana da tsarki a wurin Allah. Har da ran yaron da yake cikin uwarsa yana da tamani ga Jehovah. Kashe wannan tayin da gangan laifi ne a gaban Allah.—Fitowa 21:22, 23; Zabura 127:3.
2. Kiristoci na gaskiya suna damuwa da kiyaye lafiyarsu. Suna tabbata cewa motocinsu da gidajensu ba su da abin haɗari. (Kubawar Shari’a 22:8) Bayin Allah ba sa wasa da ransu don nishaɗi ko don murna. Saboda haka ba sa yin wasanni da ake ji ma wasu rauni da gangan. Suna guje ma nishaɗi da ke ƙarfafa yin faɗā.—Zabura 11:5; Yohanna 13:35. 3. Ran dabba ma yana da tsarki a gaban Mahalicci. Kirista zai iya kashe dabbobi domin abinci ko kuma yin tufafi ko don ya tsare kansa daga ciwo da haɗari. (Farawa 3:21; 9:3; Fitowa 21:28) Amma laifi ne a wulaƙanta dabbobi ko kuwa a kashe su don wasanni ko nishaɗi.—Misalai 12:10. 4. Shan tabā, tauna tabar baki, da kuma shan ƙwayoyi ba halayen Kiristoci ba ne. Waɗannan ayyukan ba su da kyau domin (1) suna mai da mu bayinsu, na (2) suna yi mana lahani a jiki, na (3) ba su da tsabta. (Romawa 6:19; 12:1; 2 Korinthiyawa 7:1) Yana da wuya ƙwarai a daina waɗannan halayen. Amma tilas ne mu yi haka domin mu faranta wa Jehovah rai. 5. Jini ma yana da tsarki a gaban Allah. Allah ya ce kurwa, ko rai, yana cikin jini. Saboda haka, ba shi da kyau a ci jini. Ba daidai ba ne kuma a ci naman dabba da ba a yanka ba. Idan an murɗe dabba ko kuwa ta mutu a tarko, bai kamata a ci ba. Idan aka harɓi dabba ko kuma aka soke ta, idan za a ci, to dole ne a yanka ta da sauri.—Farawa 9:3, 4; Leviticus 17:13, 14; Ayukan Manzanni 15:28, 29. 6. Daidai ne a karɓi ƙarin jini? Ka tuna, Jehovah yana bukatar mu hanu daga jini. Wannan yana nufin cewa bai kamata mu karɓi jinin wasu mutane ba ko kuwa jininmu da aka ajiye ta kowane hali. (Ayukan Manzanni 21:25) Saboda haka, Kiristoci na gaskiya ba za su amince a ƙara masu jini ba. Za su amince da wasu hanyar magani na asibiti, kamar karɓan wasu magungunan da babu jini a cikinsu. Suna so su rayu, amma ba za su karya dokar Allah ba wajen ƙoƙarin su ceci kansu.—Matta 16:25. |
||
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|