| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 10 |
Ayyukan da Allah Ba Ya So |
|
| Yaya ya kamata ka ji game da abubuwan da Allah ya ce ba su da kyau? (1) | |
| Waɗanne irin halayen jima’i ne ba su da kyau? (2) | |
| Yaya ya kamata Kirista ya ji game da ƙarya? (3) caca? (3) sata? (3) faɗā? (4) sihiri? (5) maye? (6) | |
| Ta yaya mutum zai iya barin munanan halaye? (7) | |
1. Bayin Allah suna ƙaunar abin da ke nagari. Amma tilas ne kuma su koya ƙin abin da ke mummuna. (Zabura 97:10) Wannan yana nufin guje ma wasu ayyukan da Allah ba ya so. Waɗanne ayyuka ke nan? 2. Fasikanci: Yin Jima’i kafin a yi aure, zina, jima’i da dabba, jima’i tsakanin ’yan’uwa, da kuma luwaɗi duka zunubai ne masu tsanani a gaban Allah. (Leviticus 18:6; Romawa 1:26, 27; 1 Korinthiyawa 6:9, 10) Idan namiji da ta mace suna zama tare amma ba su yi aure ba, ya kamata su rabu ko kuwa su ɗaura aure bisa doka.—Ibraniyawa 13:4.
3. Ƙarya, Caca, Sata: Jehovah Allah ba zai yi ƙarya ba. (Titus 1:2) Mutanen da suke neman tagomashinsa dole su guji yin ƙarya. (Misalai 6:16-19; Kolossiyawa 3:9, 10) Kowace irin caca cike take da kwaɗayi. Saboda haka Kiristoci ba sa yin kowace irin caca, irinsu ƙuri’a, sukuwa, da ta kati. (Afisawa 5:3-5) Kuma Kiristoci ba sa sata. Ba sa kuma sayan kayan sata da saninsu ko kuwa su ɗauki abu ba tare da izini ba.—Fitowa 20:15; Afisawa 4:28. 4. Fushi, Faɗā: Zafin hali yakan kai ga yin faɗā. (Farawa 4:5-8) Mafaɗāci kuma ba zai zama abokin Allah ba. (Zabura 11:5; Misalai 22:24, 25) Ba shi da kyau mu ɗau fansa ko kuwa mu rama mugunta da wasu suka yi mana.—Misalai 24:29; Romawa 12:17-21. 5. Makaru da Kuma Sihiri: Wasu mutane suna neman sa’a daga wurin aljanu don su warkar da cuttutuka. Wasu suna harba makaru ga abokan gabansu don su naƙasa su ko kuma su kashe su. Dukan irin waɗannan ayyukan, Shaiɗan ne yake goyon bayansu. Saboda haka kada kowane Kirista ya yi irin waɗannan abubuwan. (Kubawar Shari’a 18:9-13) Zama kusa da Jehovah ita ce kāriya mafi-kyau da za mu samu daga makaru da za a harbe mu da shi.—Misalai 18:10. 6. Maye: Ba laifi ba ne a sha ruwan anab, giya, ko wata barasa kaɗan. (Zabura 104:15; 1 Timothawus 5:23) Amma yawan shan giya da maye ba shi da kyau a gaban Allah. (1 Korinthiyawa 5:11-13; 1 Timothawus 3:8) Shan giya da yawa zai iya ji maka rauni kuma ya ɓata maka iyali. Zai iya sa ka fāɗa cikin wasu jarabobi nan da nan.—Misalai 23:20, 21, 29-35. 7. Mutanen da suke yin abubuwan da Allah ya ce ba su da kyau ba za su “gāji mulkin Allah ba.” (Galatiyawa 5:19-21) Idan kana ƙaunar Allah da gaske kuma kana son ka faranta masa rai, to, ka rabu da waɗannan ayyuka. (1 Yohanna 5:3) Ka koyi ƙin abin da Allah ya ce ba shi da kyau. (Romawa 12:9) Ka yi cuɗanya da mutane da suke da halaye masu kyau. (Misalai 13:20) Cuɗanya da ƙwararrun Kiristoci za ta iya zama hanyar taimako. (Yaƙub 5:14) Fiye da haka, ka dogara ga taimakon Allah ta wurin addu’a.—Filibbiyawa 4:6, 7, 13. |
||
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|