| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 5 |
Menene Nufin Allah ga Duniya? |
|
| Me ya sa Jehovah ya halicci duniya? (1, 2) | |
| Me ya sa duniya yanzu ba aljanna ba ce? (3) | |
| Me zai faru ga miyagun mutane? (4) | |
| Me Yesu zai yi nan gaba ga marasa lafiya? tsofaffi? da kuma matattu? (5, 6) | |
| Me ya kamata ka yi, don ka sami albarka da ke zuwa a nan gaba? (7) | |
1. Jehovah ya halicci wannan duniyar domin ’yan Adam su ji daɗin zama a cikinta har abada. Yana son mutane masu adalci, masu farin ciki su zauna a duniya ko da yaushe. (Zabura 115:16; Ishaya 45:18) Duniya ba za ta taɓa halaka ba; za ta kasance har abada.—Zabura 104:5; Mai-Wa’azi 1:4. 2. Kafin Allah ya yi mutum, Ya zaɓi wani ƙaramin ɓangare na duniya ya mayar da shi kyakkyawar aljanna. Ya kira shi gonar Adnin. A nan ne ya ajiye namiji da ta mace na farko, Adamu da Hawa’u. Allah ya nufe su su haifi ’ya’ya su cika dukan duniya. A hankali su mayar da dukan duniya ta zama aljanna.—Farawa 1:28; 2:8, 15.
3. Adamu da Hawa’u sun yi zunubi da suka taka dokar Allah da gangan. Saboda haka, Jehovah ya kore su daga gonar Adnin. An yi hasarar Aljannar. (Farawa 3:1-6, 23) Amma Jehovah bai manta da nufinsa ga duniyar nan ba. Ya yi alkawarin cewa zai mayar da ita aljanna, inda ’yan Adam za su zauna har abada. Ta yaya zai yi wannan?—Zabura 37:29. 4. Kafin wannan duniyar ta zama aljanna, tilas ne a cire miyagun mutane. (Zabura 37:38) Hakan zai faru a Armageddon, watau yaƙin Allah na kawar da mugunta. Bayan haka, za a ɗaure Shaiɗan na shekara 1,000. Wannan ya nuna cewa ba za a bar wasu miyagu su lalata duniya ba. Mutanen Allah ne kawai za su tsira.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 20:1-3. 5. Sa’annan Yesu Kristi zai yi Sarauta bisa wannan duniya na shekara 1,000. (Ru’ya ta Yohanna 20:6) A hankali zai kawar da zunubi daga zukatanmu da kuma jikunanmu. Za mu zama kamiltattun mutane kamar yadda Adamu da Hawa’u suke kafin su yi zunubi. Daga lokacin ba za a sake ciwo, tsufa, ko mutuwa ba. Marasa lafiya za su warke, tsofaffin mutane za su sake zama matasa.—Ayuba 33:25; Ishaya 33:24; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4. 6. A lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu, ’yan Adam masu aminci za su yi aiki domin mai da dukan duniya ta zama aljanna. (Luka 23:43) Kuma, za a tashe miliyoyin matattu zuwa rai bisa duniya. (Ayukan Manzanni 24:15) Idan suka yi abin da Allah yake bukata a garesu, za su zauna a duniya har abada. In ba haka ba kuma, za a halaka su har abada.—Yohanna 5:28, 29; Ru’ya ta Yohanna 20:11-15. 7. Da haka za a cika ainihin nufin Allah ga duniya. Za ka so ka sami waɗannan albarka na nan gaba? Idan kana so, kana bukatar ka ci gaba da koyo game da Jehovah kuma ka yi biyayya ga bukatunsa. Halartan taro a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehovah zai taimake ka ka yi haka.—Ishaya 11:9; Ibraniyawa 10:24, 25.
|
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|