Dandalin Halal na Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Contact Us Publications Languages
Menene Allah Yake Bukata a Garemu? Darasi na 2Talifa na bayaTalifi na gaba

Wanene Allah?

Wanene Allah na gaskiya, kuma menene sunansa? (1, 2)
Wane irin jiki ne yake da shi? (3)
Waɗanne ne halayensa na musamman? (4)
Ya kamata mu yi amfani da siffofi da alamu cikin bautarmu gareshi? (5)
Ta waɗanne hanyoyi biyu ne za mu iya mu koya game da Allah? (6)

1. Mutane suna bauta wa abubuwa da yawa. Amma Littafi Mai-Tsarki ya gaya mana cewa Allah na GASKIYA ɗaya ne kaɗai. Ya halicci dukan abubuwan da ke sama da kuma ƙasa. Domin ya ba mu rai, Shi kaɗai ne ya kamata mu yi wa bauta.—1 Korinthiyawa 8:5, 6; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

2. Allah yana da laƙabi da yawa amma sunansa na gaskiya ɗaya ne kawai. Wannan sunan shi ne JEHOVAH. A cikin yawancin Littafi Mai-Tsarki an cire sunan Allah kuma an sake sunan da laƙabi kamar su UBANGIJI ko kuwa ALLAH. Amma lokacin da aka rubuta Littafi Mai-Tsarki, sunan Jehovah ya bayyana sau 7,000!— Fitowa 3:15; Zabura 83:18.

3. Jehovah yana da jiki, amma ba kamar namu ba. “Allah Ruhu ne,” in ji Littafi Mai-Tsarki. (Yohanna 4:24) Ruhu wani irin rai ne da ya fi namu girma sosai. Babu ɗan Adam da ya taɓa ganin Allah. Jehovah yana sama, amma yana ganin dukan abubuwa. (Zabura 11:4, 5; Yohanna 1:18) To, menene kuma ruhu mai-tsarki? Ba wani ne kamar Allah ba. Amma, ikon da Allah ke aiki da shi ne.—Zabura 104:30.

4. Littafi Mai-Tsarki ya bayyana mana mutumtakar Jehovah. Ya nuna cewa halayensa na musamman su ne ƙauna, shari’a, hikima, da kuma iko. (Kubawar Shari’a 32:4; Ayuba 12:13; Ishaya 40:26; 1 Yohanna 4: 8) Littafi Mai-Tsarki ya kuma gaya mana cewa yana da jinƙai, alheri, gafartawa, mai kyauta ne, kuma mai haƙuri. Mu, kamar yara masu biyayya, ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi kwaikwayonsa.—Afisawa 5:1, 2.


Muna koya game da Allah daga halittu da kuma daga cikin Littafi Mai-Tsarki

5. Ya kamata mu yi sujjada ko kuwa mu yi addu’a ga siffofi, hotuna, ko kuwa alamu cikin bautarmu? A’a! (Fitowa 20:4, 5) Jehovah ya ce dole ne mu bauta masa shi kaɗai. Ba zai raba ɗaukakarsa da kowa ko kuwa wani abu ba. Siffofi ba su da iko su taimake mu.—Zabura 115:4-8; Ishaya 42:8.

6. Ta yaya za mu zo ga sanin Allah sosai? Hanya ɗaya ita ce ta wajen lura da abubuwan da ya halitta da kuma ta wurin yin bimbini game da abin da suke fahimtar da mu. Halittun Allah suna nuna mana cewa yana da iko da kuma hikima sosai. Muna ganin ƙaunarsa cikin dukan abubuwan da ya yi. (Zabura 19:1-6; Romawa 1:20) Wata hanya da za mu iya koya game da Allah ita ce ta wajen nazarin Littafi Mai-Tsarki. A ciki ya gaya mana ƙarin abubuwa game da yadda Allah yake. Ya kuma gaya mana game da ƙudurinsa da kuma abin da yake so mu yi.—Amos 3:7; 2 Timothawus 3:16, 17.

 

An Wallafa a Shekara ta 1996

GidaSamaTalifa na bayaTalifi na gaba

Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.