| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 1 |
Yadda Za Ka San Abin da Allah Yake Bukata |
|
| Littafi Mai-Tsarki na ɗauke da wane muhimmin bayani? (1) | |
| Wanene mawallafin Littafi Mai-Tsarki? (2) | |
| Me ya sa ya kamata ka yi nazarin Littafi Mai-Tsarki? (3) | |
1. Littafi Mai-Tsarki kyauta ce mai tamani daga Allah. Ya yi daidai da wasiƙa daga uba zuwa ga ’ya’yansa da yake ƙauna. Ya gaya mana gaskiya game da Allah—yadda yake da kuma mizanansa. Ya bayyana mana yadda za mu jure wa matsaloli da kuma yadda za mu sami farin ciki na gaske. Littafi Mai-Tsarki ne kaɗai ya gaya mana abin da ya wajaba mu yi don mu faranta wa Allah rai.—Zabura 1:1-3; Ishaya 48:17, 18.
2. Maza 40 ne suka rubuta Littafi Mai-Tsarki a cikin shekara 1,600, kamawa daga shekara ta 1513 K.Z. Yana da tarin ƙananan littattafai 66 a cikinsa. Allah ne ya hure waɗanda suka rubuta Littafi Mai-Tsarki. Sun rubuta tunaninsa ne, ba nasu ba. Saboda haka Allah da yake sama ne, Mawallafin Littafi Mai-Tsarki, ba wani ɗan Adam da yake duniya ba.—2 Timothawus 3:16, 17; 2 Bitrus 1:20, 21. 3. Allah ya tabbata cewa an kofe Littafi Mai-Tsarki daidai kuma an adana shi da kyau. An buga Littafi Mai-Tsarki da yawa fiye da kowane littafi. Ba kowa ne zai yi farin ciki ba idan ya gan ka kana nazarin Littafi Mai-Tsarki, amma kada ka bari wannan ya hana ka yin haka. Rayuwarka ta har abada ta dangana ne ga sanin Allah da kuma yin nufinsa ko ana hamayya ma.—Matta 5:10-12; Yohanna 17:3. |
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|