Shaidun Jehovah—Su Wanene ne Su? Menene Suka Gaskata? |
Menene Suka Gaskata?SHAIDUN JEHOVAH sun gaskata da Maɗaukaki Allah, Jehovah, Mahaliccin sama da ƙasa. Abubuwa masu wuya da suke wanzuwa, da ke na al’ajabi a duniya da suka kewaye mu sun nuna cewa Mahalicci mai basira da kuma iko ne ya yi su duka. Yadda ayyukan maza da mata ke nuna halayensu, haka ma na Jehovah Allah suke nuna nasa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ‘tun halittar duniya al’amura nasa da ba su ganuwa, ta wurin abubuwa da an halitta ana ganinsu.’ Haka ma, ba tare da murya ba ko kuma kalmomi ‘sammai suna bayana ɗaukakar Allah.’—Romawa 1:20; Zabura 19:1-4.
Mutane ba sa mulmula tukwanen ƙasa ko kuma su yi telibijin da kwamfita ba tare da wani dalili ba. Halittar duniya ta tsiro da ta dabbobi sun fi ban mamaki. Ba za mu iya gane yadda aka yi jikin mutum da biliyoyin ƙwayoyin gina jiki ba—ƙwaƙwalwa ma da muke yin tunani da ita aba ce ta ban al’ajabi! Idan mutane suna da dalilin da ya sa suka ƙera abubuwa da ba su da muhimmanci, hakika Jehovah Allah yana da dalilin halitta da ya yi, masu ban mamaki! Misalai 16:4 ya ce “Ubangiji ya halicci kowane abu domin nufin kansa.”
Jehovah yana da dalilin da ya sa ya yi duniya, yadda ya gaya wa mutane biyu na fari: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya . . . ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari, da kowane abu mai-rai wanda ke rarrafe a ƙasa.” (Farawa 1:28) Domin sun yi rashin biyayya, wannan mata da miji sun kasa cika duniya da iyalai masu adalci da za su kula da duniya da tsire-tsire da dabbobinta da kyau. Amma kasawarsu ba ta sa nufin Jehovah ya susuce ba. Shekaru dubbai daga baya, aka rubuta: “Allah; mai-sifanta duniya . . . , ya halicce ta ba wofi ba.” Ya “kamanta ta domin wurin zama.” Ba za ta halaka ba, amma “duniya kuwa ta dawwama.” (Ishaya 45:18; Mai-Wa’azi 1:4) Za a gano nufin Jehovah game da duniya: “Ƙudurina za ya tabbata, zan kuma cika dukan nufina.”—Ishaya 46:10.
Saboda haka, Shaidun Jehovah suka gaskata cewa duniya za ta kasance har abada, kuma dukan mutane rayayyu da matattu, da za su jitu da nufin Jehovah game da duniya mai kyau za su zauna a cikinta har abada. Dukan mutane sun gaji ajizanci daga Adamu da Hauwa’u, saboda haka dukan mutane masu zunubi ne. (Romawa 5:12) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Hakkin zunubi mutuwa ne.” “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba.” “Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu.” (Romawa 6:23; Mai-Wa’azi 9:5; Ezekiel 18:4, 20) Ta yaya za su rayu kuma su sami albarka ta duniya? Sai ta hadayar fansa na Kristi Yesu, gama ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya bada gaskiya gareni, ko ya mutu, za shi rayu.” “Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29; 11:25; Matta 20:28. Yaya wannan zai faru? An yi bayani cikin “bishara ta mulkin,” da Yesu ya soma yi lokacin da yake duniya. (Matta 4:17-23) A yau Shaidun Jehovah suna yin wa’azin bishara a hanya ta musamman. | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ABIN DA SHAIDUN JEHOVAH SUKA GASKATA
| ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
An Wallafa a Shekara ta 2000 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|